Kungiyar kwadago ta TUC ta yi martani kan shirin da ake yi na kara kudin man fetur a Nigeria, yayin da kudin gangar danyen mai ta koma $60 a kasuwar saye da sayar da danyen mai ta duniya.
Kungiyar TUC ta yi mamakin yadda gwamnatin tarayya ta yi saurin yanke hukuncin kan karin kudin man fetur din, amma ta dauki watanni ba tare da ta cika alkawarin da ta daukar wa kungiyoyin kwadago ba.
A cewar kungiyar TUC, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari mai ci a yanzu ba ta tausayin talaka ko kadan.
A cikin wata sanarwa mai dauke da taken, ‘Me ya sa kuke gaggawar sanar da karin kudin man fetur?’ kungiyar TUC ta caccaki jami’an gwamnati na rikon sakainar kashi ga lamuran da za su kawo ci gaba ga ‘yan Nigeria.
Sanarwar wacce ke dauke da sa hannun Comrade Quadri Olaleye, shugaban kungiyar TUC, ta ce: “Kungiyar kwadago ta TUC ta nuna kaduwarta kan yadda ministar man fetur a cikin karamin lokaci na tashin danyen mai a kasuwar duniya, har ta sanar da yiyuwar karin kudin man fetur a Nigeria.
“Tambayar ita ce me ya sa gwmanati ke saurin fadin karin kudin man fetur bayan karin kudin danyen mai a kasuwar duniya, amma ya na daukarsu makonni ko watanni kafin su cika alkawarin da suka daukarwa kungiyoyin kwadago? Duka hakan ya na nuni da abu daya ne kawai: Ba sa tausayin talakan wannan kasar.
“A cikin wata sanarwa da jami’an gwamnati za su fitar, za ka taras cewa suna nuna halin ko in kula da halin da ‘yan Nigeria suke ciki ko za su iya shiga.
“Kamar gwamnati mai ci a yanzu ba ta damu da talauci da rashin ayyukan yi da ta jefa ‘yan Nigeria a ciki ba, ga uwa uba matsalar rashin tsaro, da tsare tsaren gwamnatin ya jawo a cikin kasar. Babu wani abun hankali da zai dauka cikin kalaman Ministar.