Kungiyoyin da ke buga gasar kofin zakarun Turai na UEFA na shirin komawa domin ci gaba da buga gasar.
A mako na sama ne daga ranar 16 ga wannan wata da muke cikin ne kungiyoyi da suka samu tikitin shiga gasar da suka hada da RB Liepzig da za ta kece reni da Liverpool, PSG za ta fafata da Barcelona.
Ranar 17 ga wannan wata da muke cikin sa ne FC Porto za ta kece reni da Juventus,Yayin da Sevilla za ta fafata da Borussia Dortmund.
Bakin dayan su masu horar da wadanan kungiyoyi, kama daga Bajamushe Julian Nagelsmann mai horar da RB Liepzig, Jurgen Klopp na Liverpool, Mauricio Pochetino na PSG, Ronald Koeman na Barcalona, Segio Conceicao na FC Porto, Andrea Pirlo na Juventus, Julien Lopetegui na Sevilla sai Edin Terzic daga Borussia Dortmund sun dau hanyar ganin kungiyoyin su sun samu nasarori a wannan gasa.