By Ishaq Dabai
Karamar ministar babban birnin tarayya, Dakta Ramatu Aliyu, ta yi kira da a kawo canji a harkokin kananan hukumomi a kasar nan.
A cewarta, gwamnatocin jihohi suna sarrafa kananan hukumomi don dacewa da muradun su na siyasa.Ramatu tace dole ne a kara wa kananan hukumomin karfi, inda ta kara da cewa suna da matukar muhimmanci wajen cike gibin dake tsakanin matakan siyasa da abubuwan dake cikin gida don daidaita martanin a cikin dabarun ci gaban COVID-19.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mataimakiyarta ta musamman kan harkokin yada labarai, Austine Elemue, ta fitar ranar Lahadi.
An jiyo ministan tana fadar haka yayin da take gabatar da takarda mai taken, ‘Zuwa Ci Gaban Dorewa ga Ƙananan Hukumomi ga annobar Cutar ta Najeriya: Darussa daga Ƙasar Ingila,a wani taro da aka gudanar a Ƙasar Ingila ranar Asabar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “Dakta Ramatu ta lura cewa ƙananan hukumomi na iya samun damar isa ga jama’a tare da kula da cututtuka daban -daban da ayyukan tsaro na zamantakewa a lokutan wahala da ba a taɓa gani ba. Don haka, ta bada shawarar a ƙarfafa ƙananan hukumomi a cikin ikon su na mayar da martani, koyo da rage tasirin tashe -tashen hankula.
“Ministan ta kuma yi kira da a sake fasalin ayyukan kananan hukumomi a Najeriya inda gwamnatocin jihohi ke da babban tasiri da iko kan kananan hukumomi don dacewa da muradunsu da manufofinsu na siyasa.