Dan wasan baya Sagio Ramos ya rattabawa kungiyar kwallon kafa ta PSG hannu har na tsawon shekara biyu.
Ramos mai kimanin shekaru 35, yabar Real Madrid inda kwantiragin sa zai kare a June 30, bayan Kungiyar ta Madrid taki Kara masa kwantiragi. Kamar yadda Jaridar Punch ta wallafa
Wannan ya kawo karshen zaman sa a Kungiyar ta Real Madrid bayan ya shafe shekaru 16 a kungiyar.
KARANTA:- BABBAR MAGANA: An garkame masu gadi kan laifin satar kayan ma’aikata
“Ina matukar farin ciki da na dawo wannan kungiyar ta PSG” kamar yadda Dan wasan yace.
Ya cigaba da cewa “wannan babbar dama ce a gareni, kuma na bude wani shafi a rayuwa ta, wanda bazan taba mantawa dashi ba.”
Ramos din ya bukaci da ya rattabawa PSG hannu na tsawon shekara biyu, inda kudaden da zai karba a Kungiyar ta PSG bai kai wanda yake karba a Kungiyar ta Madrid,.
Ramos yace “ban taba tunanin zanbar Kungiyar ta Madrid ba,” bayan Yarjejeniyar kara masa shekara daya yayi nufin karba, sai dai kuma daga baya sai kungiyar tace masa ta fasa.
Ramos yace “Bawai matsalar kudi bane, sun bani shekara daya ni kuma biyu nake bukata,”
Za’ai bikin tafiyar sa a 17 ga watan July,
Naseer Al-Khelaifi, Mai Kungiyar ta PSG cewa yayi ” A yau Kungiyar PSG ta dauka daya daga cikin fitattun Yan Kwallon duniya na wannan zamani, muna farin cikin sanar daku Dan wasa Sagio Ramos ya shigo cikin mu, Sagio Ramos cikakken Dan wasa ne, Kuma kwararre ne a wasan baya.”
Tun daga farko dai kungiyoyi uku suka nemi daukar Dan wasan, wadanda suka hada da Manchester city, Paris Saint German da kuma Bayern Munich.