Wasu mutum shida da ke jinyar cutar korona a Abuja sun sake warkeqa kuma an sallame su bayan gwaji ya nuna ba sa dauke da cutar.
Ministan Birnin Tarayya Abuja ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter a ranar Asabar, inda ya ce adadin wadanda suka warke baki daya a garin na Abuja sun zama 46 ya zuwa karfe 10:00 na safiyar Asabar.
Mohammed Musa Bello ya jinjina wa ma’aikatan lafiya “bisa jajircewarsu” sannan ya ce suna kara azama a yaki da cutar.
Ya zuwa daren ranar Asabar mutum 343 ne suka kamu da cutar korona a Abuja.