Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ebonyi ya bayyana rahoton wani bidiyo da yake yawo ana yada cewa ana kai wa Fulani hari tare da tursasa musu su bar jihar a matsayin ‘karya’ da kuma rashin inganci.
Philip Maku, Kwamishinan ‘yan sandan shi ne ya tabbatar da hakan a sanarwar da ya fitarwa manema labarai a ranar Lahadi a garin Abakaliki.
Inda ya ce babu wanda yake korar Fulani a jihar, sannan babu wanda ya kai musu hari. Kwamishinan ‘yan sandan ya ce; a ranar 2 ga watan Janairu, wani Bafulatani makiyayi mai suna Alhaji Adamu da yake zaune a kauten Ozibo dake yankin Nkaleke Ichaba/Enyibishiri ya zabi ya sauya wurin zama.
“Adamu ya sauya wurin zama da shi da iyalinsa zuwa Taraba domin samun wurin da zai ci gaba da kiwonsa da shanunsa tunda an fara shiga rani gari ya fara bushewa”. Inji shi.
Kwamishinan ya ci gaba da cewa; Alhaji Adamu sai da ya sanar da shugaban kauyen da kuma shugaban Cibiyar ci gaban Ichaba, kafin ma ya bar inda yake cikin zaman lafiya.
“domin yaye wahami, Adamu ya tafi ya bar iyalinsa bakwai wanda ya hada da Alhaji Musa Danfo da wadansu mutum shida, wanda har yanzu suna ci gaba da zama a inda ya bari da wadansu shanu”. Ya tabbatar.
“Kafin wancan bidiyon da ya yada karya, hukumarmu ba ta da rahoton wata barazana ga rayuwar wadannan Fulani makiyaya masu son zaman lafiya ko ga shanunsu, sannan wadanda suke zama tare da su da ma al’ummar jihar baki daya wadannan Fulani makiyaya ba su zama barazana ga kowa ba”. Ya tabbatar.
Kwamishinan ya kara da cewa; yana ma da kyau al’umma ta sani cewa; a ranar 2 ga watan Janairu sabuwar shekara, al’ummar Fulani sun kai ziyarar sabuwar shekara ga Gwamna Dave Umahi, kuma babu wata barazana.
Ya ce wadanda suka saki bidiyon sun yi ne domin biyan bukatar kawukansu da haddasa rikici da fitina tare da sauya tunanin mutane. Inda ya ce kuma rundunarsu za ta yi bincike kan lamarin domin cafko wadanda suka yada wannan bidiyon.