Hukumar da ke lura da tattara bayan ‘yan kasa, NIMC ta karyata rahoton da ke cewa an yi wa shafin hukumar kutse, inda aka rasa wadansu bayanai.
Kakakin hukumar, Kayode Adegoke ne ya karyata hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, inda ya ce rahoton cewa an yi wa shafin kutse kuma labarin ya rika yawo a shafukan sada zumunta, to tabbas karya ne. Ya ce yada hakan suna yi domin kawo tsaiko a ci gaba da rijistar da ake yi.
NIMC sun ce babu wani abu makamancin haka da ya faru. Ya ce a binciken da suka yi, sun gano cewa wadanda suka yada cewa babu bayanansu a shafin NIMC din, dama can babu bayanan na su ne. Domin ba su yi rijista ba.