Gwamnatin tarayya ta bayyana irin dabaru da za ta bi wajen ganin ta tara kudi kimanin dalaq biliyan daya da rabi don aikin matatar man Fatakwal.
Karamin Ministan Man Fetur na tarayya Timipre Sylva shi yab bayyana haka inda ya ce daga cikin dala biliyan daya da rabin gwamnati za ta cire dala miliyan dari takwas daga kasafin shekrar 2020 zuwa shekara ta 2022.
Sylva wanda ya bayyana haka wa tasahr Talabijin na Channels ya ce Kamfanin mai na NNPC kuma zai bada naira miliyan dari biyu daga kudaden shigar shi.
Ya ce “Akwai ayar tambaya da ake ta dasa mana kan cewa, yaushe ne za mu yi garan bawul ga matatun man mua, yaushe ne za mu inganta matatun man mu? a halin d ake ciki muna ci gaba da yin aikin matatun man, to amma dole ne suna buktar kudade”
Ya ci gtaba da cewa “Bari na fada muku wani irin dabara muke yi gurin aikin matattun man, ba wai kawai za mu ciyo bashi ba ne kan aikin kacokam, ba kawai za mu raja’a ne kan basussuka ba”.
“Kasafin kudin 2020 zai bada dala miliyan dari uku da hamsin, 2021 shi ma zai bada dala miliyan dari uku da hamsin, yayin da 2022 kuma aza mu cire dala miliyan dari inda haka ne ya hadu ya zama dala miliyan dari takwas. cewar Timpre Sylva.