By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin ta da gwamnatin kasar Burkina Faso domin dakile tare da murkushewa da kuma hukunta masu safarar bil’adama musamman mata da kananan yara.
A cikin wata sanarwa a ranar Lahadi mai taken, ‘Gwamnatocin Najeriya da Burkina Faso sun nuna aniyar siyasa ta yaki da safarar mutane, kan sanya hannu a yarjejeniyar MOU,’ Jami’in yada labarai na Hukumar Yaki da Fataucin Bil Adama ta kasa, Adekoye Vincent, yace an sanya hannu kan sabuwar dokar ta kasa da kasa ne a Abuja, a wata muhimmiyar hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Burkina Faso karo na uku da aka gudanar a otal din Transcorp Hilton, dake Abuja.
A cewarsa, yarjejeniyar ta MOU da ake sa ran zata kara tsananta matsin lamba kan masu safarar mutane da kungiyoyinsu dake aiki a cikin kasashen biyu na zuwa ne makonni masu zuwa bayan da aka kulla irin wannan yarjejeniya tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Nijar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Jakadan Najeriya a Burkina Faso Mistura Abdulkareem ne ya sanya hannu a takardar a madadin gwamnatin Najeriya da kuma jakadan Burkina Faso a Najeriya, Piabie N’DO ya sanya wa hannu a madadin kasar Burkina Faso.
Da take jawabi a wajen rattaba hannun, Darakta-Janar ta Hukumar NAPTIP, Dakta Fatima Waziri-Azi, tace yarjejeniyar ta ci gaba da zama babbar barazana ga ayyukan masu safarar mutane ba wai a cikin hanyoyin kasashen biyu kadai ba, har ma da yammacin Afirka baki daya.
Sannan ta godewa shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), da ministar harkokin jin kai, da al’amuran bala’o’i da ci gaban jama’a, Sadiya Farouk, ministar harkokin waje da sauran masu ruwa da tsaki na jiha da wadanda ba na jiha ba bisa nuna aniyar siyasa ta magance matsalar yaki da fataucin mutane.
A nasa jawabin, babban sakataren ma’aikatar harkokin wajen kasar, Gabriel Aduda ya bayyana cewa, yarjejeniyar wani bangare ne na kokarin da gwamnatin tarayya take yi na inganta hadin gwiwa da karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Kazalika ya kuma tabbatar wa masu ruwa da tsaki cewa za a aiwatar da abubuwan da ke kunshe cikin sabuwar yarjejeniyar ta MoU daidai da ka’idojin da aka amince da su.
Ita ma a nata jawabin, Darakta-Janar na hadin gwiwa a Burkina Faso, Misis Bakyonon Kanzie, ta godewa gwamnatin tarayya bisa wannan yarjejeniya, inda tace kasarta za ta aiwatar da dukkan bangarorin yarjejeniyar domin amfanin Najeriya da Burkina Faso.
Ta kara da cewa, “MoU ya samo asali ne daga damuwa game da girma da kuma barazanar fataucin mutane, musamman mata da kananan yara a kasashen biyu da kuma mummunan tasirinsa na zamantakewa da tattalin arziki ga rayuwar ‘yan kasarsu.
Sannan “Sake tabbatar da cewa himma da wajibcin da bangarorin biyu ke da shi na aiwatar da shirin kungiyar ECOWAS na yaki da fataucin mutane na shekarar 2002-2003 da kuma wadannan dokoki na kasa da kasa sun amince dasu.