Katsina: Hukumar Kiyaye Haɗurra FRSC tace zata hukunta Direbobin da basu Balaga ba
Shugaban Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa reshen Jahar Katsina Ali Sule yace Kotun tafi da gidan ka ta Hukumar zata hukunta duk wanda aka kama yana tuƙi mai kananan shekaru a Jahar.
Sule ya bayyana haka ga Manema labaru a ranar Lahadi a Katsina.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sanata Uba Sani ya taya Al’ummar Musulmi murnar shaida Babbar Sallah ta bana
“Hukumar zata duba a matsayin Babbar laifi duk wani yaro da aka kama yana tuƙi a Babbar hanya a Jahar.
“Idan muka kama duk wani yaro mai kananan shekaru, zamu miƙa shi ga Kotun tafi da gidan ka, domin zartar mashi da hukunci,” Inji shi.
Kwamandan ya shawarci Iyaye dasu daina barin kananan yara suna tuka motoci a manyan hanyoyin Jahar.
Haka zalika, Kwamandan yayi kira ga Direbobi dasu tabbatar sun yi tuƙi mai kyawu a lokacin daminar nan ta bana.
A cewar sa, dole su tabbatar suna da abin goge ruwa na gilashi Wipers, da tayoyi masu nagarta, da haske, da dukkanin abubuwan da zasu taimaka masu wajen tuki a cikin ruwa a lokacin Damina.
Ya yi kira a garesu dasu tabbatar sun bi dukkanin ƙaidojin tuƙi.