A jiya ne aka yi Taron zuba Hannun jari a jihar Kaduna a Karo na 6 wanda mataimakin shugaban Kasa ya hallatta, Dayake jawabinsa Sanata Uba Sani, kuma Sanatan Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijan Nageriya ya ce, Tun da sanyin safiyar jiya Alhamis:
“Nabi sahun Mataimakin Shugaban Ƙasa, ƙwararren masani kuma Farfesa Yemi Osinbajo da jagora na, kuma maigidana mai kwazo Gwamna Nasir El-Rufai da sauran manyan mutane a babban Taron Zuba hannun Jari ga jihar Kaduna a Karo na Shida 6 Mai taken #KADINVEST 6.0, da Kuma binkin ƙaddamar da sabuwar Kasuwar Kasuwan Magani a karamar hukumar Kajuru”
Sanata Uba Sani ya Kara da Cewa, Gwamna Malam Nasiru El-Rufai, tun lokacin da ya hau karagar mulki a shekarar 2015, ya ba da fifikon ga tsarin, domin sake dawo da martabar tattalin arzikin jihar ta Kaduna, inda ya kafa tsarin doka da ta hukumomi, Wanda yanzu Haka Jihar Kaduna ta Zama abar koyi cikin Sauki a fannin Kasuwanci.
Ya Kuma ce, “Jihar ta Kasance ita ce babbar hanya mafi kyau ga masu saka jari. Taron saka hannun jarin na Kaduna babban jigo ne na canjin tsarin tattalin arziƙin gwamnatin El-Rufai. Ina goyon bayan jagoranmu masoyinmu kan wannan ci gaban, tabbas wannan tsari na KADINVEST shine alamar jagoranci na mai hangen nesa.”
“Madallah da Godiya ta musamman ga Gwamna Malam El-Rufai Sakamakon daukar kwararan matakai Duk domin warkar da tsofaffin raunuka da mayar da wannan yanki dake fuskantar kalubalen tafarkin ci gaba da wadata musamman a wannan lokacin kaddamar da Kasuwar Kasuwan Magani dake, Karamar Hukumar Kajuru” inji Sanata Uba Sani.
Kazalika ya Kuma ce, “Shugabanmu masoyinmu Gwamna El-Rufai ya samu tarba Mai cike da kauna a fuskoki Masu cike da murna daga mutanen Kasuwan Magani. Manyan jami’an gwamnatin tarayya da na gwamnatin jihar Kaduna sun yi Matukar murna ga wannan bikin kaddamar da kasuwar”
“A nawa bangaren A cikin sakon fatan alheri na, na bayyana cewa kaddamar da Kasuwar Kasuwan Magani da ke karamar hukumar Kajuru wani muhimmin ci gaba ne a cikin ayyukan da Gwamna El-Rufai ke yi a jihar Kaduna. Ya canza fuskar zamantakewar tattalin arzikin jihar Kaduna cikin kankanin lokaci. Ana samar da damar tattalin arziki a kowace rana duk domin fitar da mutane daga talauci Wanda yanzu Haka martabar Kasuwanci na cigaba da tasowa kuma Muna cigaba da tallafawa” Inji Sanata Uba Sani.
Daga Karshe Sanatan ya rufe da kalmar cewa A madadin mutanen kirki na shiyyar sanata ta Kaduna ta tsakiya, ina gode wa gwamna El-Rufai domin bunkasa kyakkyawar kasuwa a mazabar mu, tare da Cewa wannan wata hanya ce mafi kyau ta nuna kauna ga jama’a.
Duk da haka na roki mutanenmu da su sake nuna irin wannan kyakyawan aikin na Gwamna ta hanyar yin aiki tare don tabbatar da zaman lafiya. Tare da kwanciyar Hankali, domin tabbatar da ƙarin ci gaba.