Shahararren dan wasan kwallon kafar nan, wanda yanzu haka yake kasar Italiya a kungiyar kwallon kafa ta Juventus wato Christiano Ronaldo ya bai wa al’ummar Falasdinawa Dala Miliyan 1 da Dubu dari biyar a matsayin gudummawarsa gare su.
Shahararren dan kwallon ya ba su wannan zunzurutun kudin ne a cikin wannan watan na Ramadan.
Dan wasan ya shahara wajen yin tir da haramtacciyar kasar Isra’ila bisa hare-haren da suke kai wa Falasdinawan.