KEDCO ta Ƙaryata Zargin Biyan Dubu 27,000 Kuɗin Wutar Lantarki duk Wata a Katsina
Shuwagabancin Kamfanin Rarraba Hasken Wutar Lantarki na Kano KEDCO ya ƙaryata zargin cewa dukkanin Abokanan Hulɗar sa a Jahar Katsina zasu riƙa biyan Naira Dubu 27,275.47 a matsayin Kuɗaɗen Wuta na Wata-Wata daga watan Fabrairu na Shekarar 2022.
KEDCO a cikin wata sanarwa da Shugaban ta akan Sadarwa Ibrahim Sani Shawai ya fitar a ranar Litinin, ya bayyana zargin a matsayin labarin ƙanzon kurege, marar tushe.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Harin yan bindiga a Kaduna ya sanya Tunibu ya soke taron bikin cikar sa shekaru 70
Wata Kafar Sadarwa ta kawo rahoton cewa KEDCO ta ƙara kuɗin da zata riƙa cajin Abokanan Hulɗar ta a Jahar Katsina Naira Dubu 27,275.47 daga watan Fabrairu na wannan Shekarar.
Amma a Sanarwar da Shawai ya fitar, yace “Wannan Ƙaryace, kuma muna janyo hankalin Al’umma cewa, sanarwar da wata Kafar Sadarwa ta zamani ta fitar, bai bayyana matsayar Kamfanin KEDCO ba, don haka ba gaskiya bace.
“Wannan jawabin da Kafar Sadarwa ta zamani ta fitar, maida jawabi ne ga wani Abokin Hulɗar Kamfanin, kuma ko kaɗan ba yana nufin dukkanin Abokanan Hulɗa zasu biya hakan ba.
“Akan bayanan da muka fitar a takardar da muka turawa Abokin Hulɗar mu, ya faru ne a dalilin ƙara mashi yawan wutar lantarki zuwa awanni 22 gami da canja layi daga Band C zuwa B.”
A cewar sa, “muna Son mu sanar cewa wasu Abonanan hulɗa a Katsina ana karɓar Ƙasa da Naira Dubu 10,000 a watan Fabrairu na wannan Shekarar.”
A lokacin da yake kira ga Al’umma dasu jefar da wannan jawabi, Shawai yayi kira ga Kafafen Sadarwa dasu daina “bayyana wani jawabi domin raɗin kansu”.