Wani matashi ɗan Najeriya ya fashe da kuka a wajen bikin murnar zagayowar ranar haihuwar matar sa.
Matashin ya fashe da kukan lokacin da take tuno halaccin da matar sa tayi masa lokacin da yake fama da talauci.
KU KARANTA: Aure akwai daɗi, na sha baƙar wuya lokacin da nake gwauruwa -wata budurwa
A wani bidiyo wanda shafin Yabaleftonline ya sanya kuma ya karaɗe shafukan sada zumunta, an nuna matashin yana ta hawaye lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wurin shagalin bikin zagayowar matar sa.
Da yake jinjinawa matar a gaban ƴan’uwa da abokan arziki waɗanda suka halarci wurin bikin, matashin ya jinjina mata bisa yarda da tayi da burinsa sannan ta tsaya a wajen sa lokacin da baya da ko sisi.
Ya bayyana ta a matsayin mace ƴar baiwa wacce ta tserewa sauran mata nesa ba kusa ba. Ya kuma gode mata bisa yadda ta tarbiyyantar da ƴaƴan su.
“Ba ki zaɓi bin abin duniya ba, kin bi mutumin da yake da hangen nesa, kin bi wanda yake da buri. Ta goyi baya na, ta ƙarfafa min guiwa lokacin da abubuwa suka yi tsauri. A wajena, hakan shine dalilin da ya sanya kika fi sauran mata, kin tsaya a wajena lokacin da bani da komai. A cewar sa.
Ku kalli bidiyon a nan
Yadda Wani Matashi Ya Haɗa Mota Da Sanduna, Bidiyon Ya Ɗauki Hankula
Wani mutum ya zama abin magana a manhajar Instagram bayan ya haɗa mota da sanduna sannan ya sanya mata inji.
A cikin bidiyon wanda wani shafi mai suna BCR Worldwide ya sanya a Instagram, matashin ya shiga cikin motar sannan ya tayar da ita. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Duk da cewa ba a san tsawon lokacin da ya kwashe yana ƙoƙarin haɗa sandunan domin samar da motar ba, wasu mutane da yawa sun yaba masa bisa wannan namijin ƙoƙarin da yayi.