Wani sashe na ‘yan gudun hijirar Ruwanda da ke zaune a Mozambique sun fara komawa gida bayan kusan shekaru talatin tun bayan da suka tsere daga kisan kare dangi na shekarar Alif Dari Tara da cassa’in da hudu (1994.)
Tsakanin Afrilu da Yuni shekarar 1994, an kiyasta cewa an kashe mutanen Ruwanda akalla dubu Dari takwas ( 800,000) a cikin kwanaki dari. Wasu miliyoyi kuma sun tsere zuwa kasashe makwabta.
Hukumomin Mozambique sun yi kiyasin cewa akwai ‘yan gudun hijirar Rwanda kimanin 3,000 da ke zaune a kasar.
Da yawa daga cikinsu yanzu suna ganin cewa yanayin da ya tilasta musu barin ƙasarsu ya canja.
Gwamnatin Rwanda na tallafa wa shirin mayar da ‘yan gudun hijiran. Komawar na kashin kai ne kuma a wannan makon za a dawo da wasu ‘yan gudun hijira 19 zuwa gida, a cewar gwamnatin kasar
Daya daga cikin ‘yan gudun hijirar, Miyonsenoa Domoties, ta ce tana da yakinin cewa an sami zaman lafiya a Ruwanda kuma ta komawa gida bayan ta shafe shekaru takwas a Mozambique.
“Mun zaɓi mu gudu zuwa Mozambique. Amma bayan wani lokaci, bayanai masu kyau sun zo da ke nuni da cewa akwai zaman lafiya a Ruwanda, don haka muka yanke shawarar komawa gida,” inji ta.
Kisan gillar ya samo asali ne sakamakon mutuwar shugaban kasar Rwanda Juvenal Habyarimana, dan kabilar Hutu, lokacin da aka harbo jirginsa a sararin samaniya daf da filin jirgin Kigali a ranar 6 ga Afrilun 1994.