Al’ummar Zakka da ke karamar hukumar Safana ta jihar Katsina na zaman dar-dar game da kisan da aka yi wa tsohon shugaban riko, Alhaji Hamza Abdullahi da ake zargin shi ne mai sanar da ‘yan bindiga bayanan sirri.
A cewar majiyoyin cikin gida, kisan na da nasaba da hare-haren da jami’an tsaro na Katsina suka yi a baya-bayan nan kan wasu da ake kyautata zaton masu hadin gwiwa ne ko kuma masu ba da labari da ke taimaka wa ‘yan bindiga.
Karanta nanDalibi Ya Daba Wa Malaminsa Wuka Har Lahira A Jahar Taraba
DAILY POST ta tattaro cewa jami’an tsaron Security Watch ne suka kashe Alhaji Hamza bayan samunsa da laifin kwarmata bayanai da barayin daji masu kawo hare hare a yankin.
Hare-haren da ake ci gaba da kai wa a kauyen na Zakka ya mamaye yanayin da ake ciki, lamarin da ya haifar da fargaba a tsakanin mazauna garin.
Alhaji Sani Sada, wani fitaccen dan unguwar Zakka, ya ba da labarin wani hari da aka kai masa a kwanakin baya. ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da dansa kuma sai da ya bayarda kimanin Naira miliyan 1.5 a matsayin kudin fansa kafin a sako shi.
A halin da ake ciki dai, iyalan marigayi shugaban sun yi kakkausar suka na neman a yi musu adalci, tare da nuna yatsa ga hukumar tsaro ta Security Watch.
Sai dai Imam Liman Sahalu Lawal, babban malamin addini a cikin al’umma ya musanta ikirarin da iyalan marigayi tsohon mataimakin shugaban rikon suka yi kuma sun bayyana cikakken goyon bayansu ga aiwatar da Hukumar Tsaron da Gwamnatin Jihar Katsina ta yi.
Wani mazaunin garin Zakka, Malam Yakubu Abubakar ya ce tun bayan samar da jami’an tsaro na Security Watch yanzu za mu iya yin barci kadan duk da cewa ba a rufe idanunmu gaba daya ba.
A wani labarin kumaGwamnatin Yobe Ta Karbi Rahoton Bin Manufofin Makarantu Masu Zaman Kansu
A matsayina na matashi a wannan al’umma, ina da cikakkiyar masaniyar irin halin da muke shiga a kullum kafin isowarsu cikin al’ummarmu.
Mun ji daɗin kasancewarsu a garin Zakka a yanzu. Ina so in yabawa Gwamna Malam Dikko Radda bisa jajircewarsa wajen kafa kungiyar Watch Corps ta Katsina.