Daga Suraj Na’iya Kududdufawa.
Aci gaba da fafata wasannin nahiyar turai da ƙasashe daban-daban suke fafatawa tun a tsakiyar makon daya gabata inda a daren yau ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Portugal kuma zakarun gasar za ta fafata wasa da ƙasar Sweden.
A daren yau ɗin dai akwai yiwwuwar Christiano Ronaldo ya cimma tarihin jefa ƙwallye guda 100 a ƙasar sa ta Portugal duba da yadda yake jefa ƙwallaye ko ta ina idan yana wakiltar ƙasar tasa ta Portugal.
Bisa yadda yake ƙoƙari yasa aka bashi jagorancin ragamar ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta ƙasar Portugal wato Captain kenan kuma a tarhin ƙasar babu ɗan wasan daya kafa tarihi kamar sa tunda suka fara buga ƙwallon ƙafa.
Ronaldo dai ya zuwa yanzu ya jefa wa ƙasar sa ƙwallye guda 99 inda ƙwallo ɗaya tilo yake buƙatar zurawa ya kafa tarihin jefa ƙwallye 100 inda nan bada daɗewa ba ake ganin zai karya tarihin shahararren ɗan wasan nan na ƙasar Iran da yafi kowa jefa ƙwallye.
A yanzu haka Christiano Ronaldo kofi ɗaya ne ya ragemasa bai lashe ba wato gasar cin kofin duniya da ƙasar Qatar zara karɓi baƙunci a shekarar 2022 wato nan da shekaru biyu masu zuwa, haka Portugal bata taɓa lashe gasar cin kofin duniya ba a tarihi.