Sanin kowa ne cewar duk gatan wani kamfani ko wata jaruma ko wani jarumi wajen yin fim a masana’antar shirya fina-finai ta ƙasar India da ake kira da Bollywood to gatansu itace gidajen da ake haska fina-finai wato cenema. Domin mafi yawa idan fina-finansu suka fito ana haskasu a sininu kuma hakan yana saurin sanyawa su mayar da kuɗinsu da wuri kuma har suci riba a cikin ƙanƙanan lokaci.
Idan Indiya suna haska fina-finai a sinimu to su koda yaushe haskawa sukeyi da safe da rana da yamma harma da daddare, sai dai za a iya cewa idan fa aka saki sabon fim gidajen kallon nacan ƙasar ta Indiya sai suyi sati ko sati biyu ko wata guda suna ta haska shi musamman ma idan labarin cikin fim ɗin yana da kyau da ɗaukan hankali inda daga hakan jarumi ya mai da kuɗinsa wani ma ya ninka kuɗin da ya kashe.
Sanin kowane tun bayan shigowar cutar Coronavirus data addabi al’umma komai ya samu tasgaro inda daga ciki harda ita kanta masana’antar ta Bollywood duba da yadda wasu jaruman suka fara yin aikin fim kuma suka dakatar da yin aiki da kuma sinimu na ƙasar ta Indiya suma aka kullesu, haka akwai jaruman da suka kammala aikin fim ɗinsu amma basu sakeshi ba sakamakon gudun asara.
An rufe dukkanin wasu sinimu a ƙasar India tun watanni bakwai (7) da suka gabata inda rashin haska fina-finan ba ƙaramin koma baya ya kawomusu ba musamman ‘yan kasuwa da jarjmai da kamfanonuwan da suke shirya fina-finan, sai dai itama ƙasar ta Indiya tana daga cikin jerin ƙasashen da cutar ta ragargaza sosai duba da cewar wannan cutar har wasu manyan jarumai ta kama sannan ta kama mawaƙa da sauransu inda saida aka killace su.
A yanzu dai an bayyana ranar 15 ga watan nan na Oktoba na shekarar 2020 a matsayin ranar da za a dawo domin ci gaba da kallo a dukkanin Sinimun ƙasar ta Indiya ganin cewar cutar tayi sauƙi sannan kuma a wasu ƙasashen wasu sun haƙura zasuyi rayuwa da Corona sunkama yin sabgoginsu inda suma indiyan kusan hakance ta tabbata akansu. Sai dai an bayyana cewar ba ɗari bisa ɗari za a dinga shiga kallon ba akwai tsari tunda akace kashi 50 za a dinga shiga duba da cewar akwai dokoki da hukumar lafiya ta gindaya na tsarin kallon.
Amma kuma daga jin cewar za a buɗe Sinimu a ƙasar ta Indiya tuni wasu jaruman da yawa da suka fara yin aikin fim ɗinsu suka dakatar suka bayyana cewar zasu shirya suje su ƙarasa yin fina-finan nasu, sai dai ga kaɗan daga cikin jaruman
1. Akwai jaruma Kangana Ranaut wadda ta fara aikin fim ɗinta mai suna Thalaivi wanda tayi rabi sai kuma cutar Covid 19 ta kunno kai sabo da haka dole ta dakatar da aikin fim ɗin, amma kuma tuni ta bayyana farin cikinta dataji ance za a buɗe Sinimu yayin da ta ɗaura ɗanba na ci gaba da aikin fim ɗin nata domin kammala shi.
2. Akwai shahararren jaruminnan wanda yake da barkwanci wato Akshey Kumar inda shima akwai fim ɗinsa wanda tuni ya kammala shi mai suna Bell Bottom inda a can ƙasar Scotland aka kammala aikin fim ɗin inda ana komawa kallo a sinimu zai sakeshi.
Jaridar www.dimokuradiyya.com.ng ta sami tattaunawa da Abba India Dala dake jahar Kano wanda cikakken mai bibiyar Indiya ne ako da yaushe inda yayimana ƙarin haske dangane da sake buɗe Sinimun:
“Eh to hakane sake buɗe Sinimun na ƙasar Indiya zai amfanar da ‘yan kasuwa da su kansu jaruman duba da cewar ta naan wajen sukafi samun kuɗaɗe sosai da sosai, amma ayanzu basa samin kuɗi da yawa idan basuyi anfani da sinimu ba. Sannan abu na biyu za a iya fuskantar wata matsala, matsalar kuwa itace shin idan an koma sinimun mutane zasu dinga shiga sosai? Wasu mutanen ganin yadda har yanzu akwai ragowar wannan cuta bai zama lallai su dinga shiga kallon fina-finan ba, kaga koda ansake buɗe Sinimun to akwai gagarumar matsala ta wajen sanun kuɗaɗen shiga a wajen su kansu jaruman da ‘yan kasuwa matuƙar mutane basa shiga kallon sosai”