Al’ummar garin Zaranda dake karamar hukumar Toro a Jihar Bauchi sun koka kan yadda karancin ruwan sha ya jefa su cikin mawuyacin hali.
Wannan gari dai ba shi wata tazara da fadar gwamnatin Jihar Bauchi wato Bauchi, toh amma duk da wannan kusanci, bai sa sama da mutane dubu 30 na fuskantar mummunan yanayi ba sakamakon amfani da gurbataccen ruwa.
Bayan shafe tsawon lokaci suna shan fama, al’ummar wannan gari sun fito a yau juma’a inda suka gudanar da aikin gayya don inganta Kududdufin da suke samun ruwa tun tale-tale.
A hirarsa da Jaridar Dimokuradiyya, Wakilin wannan gari na Zaranda mai suna Aliyu Yakubu, ya shaida cewa ruwan da dabbobin su ke sha nan su ma suke umumi su kai gidajen su don amfanin yau da kullum.
Ko da yake kamar yadda ya bayyana sun dade suna kai koke wa gwamnati, to amma har kawo yanzu ba a dube su da idanun rahma ba duk da irin halin wayyo Allah da suke.
Kawo yanzu dai al’ummar wannan gari sun fito duniya sun bayyana kurruwan su na neman ɗoki daga ɗaiɗaikun jama’a da ma Kungiyoyi bada tallafi da su kawo musu agaji don fitar da su daga wannan hali.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta gano cewa al’ummar wannan kauye na fama da matsanancin cututtuka na yau daban na gobe daban sakamakon amfani da Wannan ruwa na Kududdufi.