Gwamnatin tarayya ta ce an fasa komawa makaranta saboda annobar cutar Korona. Inda gwamnatin ta ce ta sauya matsayin ta na sake bude makarantu domin bai wa daliban da ke shirin kammala karatu daukar jarabawa saboda abin da ta kira “barazanar cutar korona.”
Ministan ilimi Adamu Adamu ne ya bayyana hakan, inda ya ce sakamakon wannan mataki da gwamnati ta dauka, babu wani dalibin Najeriya da zai rubuta jarabawar kammala karatun Sakandare da ake kira WAEC wanda Hukumar kula da jarabawar ta shirya gudanarwa daga ranar 5 ga watan Agusta zuwa 5 ga watan Satumba mai zuwa.
Ministan ya ce babu wani shiri na sake bude makarantun yanzu haka, saboda haka babu ranar gudanar da wannan jarabawa ta kamala karatun Sakandare bana.