Rahotanni daga gwamnatin jihar Kaduna na nuni da cewa, gwamnatin ta sanar da sabuwar doka a wani yunkuri da take yi domin ganin ta dakile yaduwar cutar Korona.
Sanarwar wacce gwamna Nasiru El-Rufai ya fitar a yau Lahadi, ta tabbatar ta takaita lokutan zuwa coci da masallaci, inda aka rage zuwa awa daya kacal.
Sannan kuma gwamnan ya ce, ma’aikatan gwamnati da ke matakin aiki na 14 zuwa kasa za su yi aiki ne daga gida daga gobe Litinin.
Wasu na hasashen cewa zai yi wahala gwamnan idan bai garkame jihar ta Kaduna ba.