Wata kungiya da ba na gwamnati ba mai suna ‘Network for Development Foundation’ ta bai wa gwamnatin Kano sinadaren wanke hannu da kuma bokitan zuba sinadaren wanke hannun a wani mataki na tallafawa wajen yaki da cutar Korona a jihar.
Hamid Ali, Sakataren kungiyar, a yayin da yake mika kayayyakin a ranar Juma’a a Kano, ya ce sun yi hakan ne a wani mataki na dakile yaduwar cutar a jihar.
Leadership A Yau ta labarto cewa; Sakataren ya ce za su sanya ababen wanke hannun ne a kasuwanni, da kuma wuraren taruwar al’umma domin ganin Korona ba ta yi tasiri a jihar ba.
Da yake maida jawabi a yayin karbar kayayyakin, Dr Kabiru Getso, Kwamishinan muhalli a jihar, ya yaba bisa wannan tallafin, inda ya ce zai taimaka wajen yaki da cutar da gwamnatin jihar ke yi.
Getso ya tabbatar da cewa tallafin kayayyakin zai riski wadanda aka bayar dominsu, inda ya ce wanke hannu yana daga cikin muhimman abu wajen dakile cutar.
Sannan ya yi kira ga kungiyoyi da daidaikun al’umma da su yi koyi da wannan kungiya wajen taimakawa wajen yaki da Korona
“Gwamnati kadai ba za iya yaki da wannan annoba ba. Akwai bukatar samun hadin guiwa daga dukkanin al’umma musamman masu hannu da shuni da kamfanoni da kuma kungiyoyi, wajen taimakawa a yaki wannnan annoba.” Inji shi.