Sakamakon dokar zaman gida da aka kakaba a kasar Afrika ta Kudu a wani mataki na dakile yaduwar cutar Korona na sama da wata guda, mabarata a kasar sun shiga halin kunci da tasku, sakamakon babu mai fitowa balle ya taimake su da wani abu na yau da kullum.
Da wannan tsattsauran, mabarata ba su samun taimako daga masu motocin da suke wucewa da kuma masu shaguna da sauran su.
Mafi yawan wadannan mabaratan da lokutan suke rayuwa cikin kunci da wahala, baki ne da suke je kasar ba su da takamaimen sana’a ko wurin zama, inda kuma suka dogara da baran da suke yi wajen samun abin da za su sanya a bakinsu.