Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa ta kasa, NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 14 da suka mutu sannan 1,617 suka kamu da annobar korona a ƙasar ranar Litinin.
Idan aka yi la’akari da sabbin alkaluman hukumar, har yanzu jihar Legas ce ke kan gaba da mutanen da suka kamu da cutar cikin kwana ɗayan inda take da mutum 776.
Jihar Kaduna ce take biye da Legas da mutum 147 sai kuma jihar Kwara da 131 da Abuja mai 102.
Jihohin da suke da mutum kasa da dari masu cutar su ne Filato-78, Edo-59, Ogun-53, Osun-45, Rivers-37, Taraba-36, Nasarawa-34 da Adamawa-33.
Sai kuma Kano-26, Delta-20, Ebonyi-16, Bayelsa-11, Gombe-11 da jihar Borno-2.
Yanzu dai kididdigar masu cutar a Nijeriya ita ce 112,004 sannan mutum 89,939 sun warke inda kuma mutum 1,449 suka rasu.