Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ce ƙwaya ce ta yi sanadin mutuwar matashiya ‘yar shekara 18 da aka tsinci gawarta a masaukin baƙin gwamnatin Yobe da ke Damaturu.
Kakakin ‘yan sandan jihar, ASP Dungus Adul-Kareem ne ya tabbatar da hakana cikin sanarwar da ya fitar, inda ya ce; bincikensu ya nuna musu cewa matashiyar mai suna Bilkisu Ali ta mutu ne sakamakon ƙwankwaɗan ƙwaya da ta yi.
A ranar 7 ga watan Janairun 2021 aka cafke mutane 4 da ake zargi da alaka da aikata kisa kan matashiyar. Sai dai an tsare su tare da mika gawarta asibiti domin binciken gano sanadin mutuwarta.
Yanzu haka dai za a mika mutanen 4 da ake zargi gaban kotu domin amsa tuhume-tuhume da ake musu wanda ya kunshi haɗa-kai wajen aikata mugun laifi da kisan-kai da zina.
Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta gargaɗi masu yaɗa jita-jita da su guji yaɗa maganganun da za su kasance matsala ga dangin yarinyar da aikin jami’an tsaro.