Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce kwamitin da shugaban kasa ya kafa don yaki da cutar korona a kasar ya yi watsi da jihar Kano duk da mawuyacin halin da jihar ta shiga.
A wata hira da BBC, Gwamna Ganduje ya ce lamarin da ake ciki a Kano yana da ban tsoro.
“Halin da ake ciki yanzu, wato muna da babbar matsala, kuma zan iya cewa da kai wannan hali a yanzu haka dai gaskiya ba shi da kyau kuma abin tsoro ne,” in ji Ganduje.
Ya ce babban abin da aka dogara da shi a kokarin dakile Korona a jihar shi ne gwaji, wanda yace an shafe kwanaki biyar zuwa shida wadanda aka dauki samufurinsu ba su san matsayinsu ba.
“Kayan da ma ake daukan (samfurin) a kai Abuja sun yi karanci, kuma ba kaya ne wanda gwamnati za ta je kasuwa ta saya ba,” a cewar Ganduje.
Ya kara “Wadanda aka dau samfurinsu ba su san matsayinsu ba. Za su ci gaba da hulda da mutane.”
Gwamna Ganduje yace “Saboda haka wannan babbar matsala ta kwamitin shugaban kasa na Abuja, shi kansa babban daraktar (hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa NCDC ya zo nan Kano ya kwana, to amma tun da ya tafi ba mu sake jin duriyarsa ba.”
To sai dai kwamitin na shugaban kasa kan yaki da cutar korona ya musanata wadannan zarge-zarge, inda ya ce suna bai wa Kano kulawa ta musamman.
“Shi ma minista (na lafiya) ya sani cewa wannan dakin gwaji ba ya aiki, amma ba mu sake jin komai ba,” a cewar gwamnan.
Gwamna Ganduje ya kara da cewa baya ga karancin cibiyoyin gwaji a Kano, jihar ba ta samun isassun kayan da za a yi gwajin da su wadanda ya ce gwamnatin tarayya ce kadai ke samar da su.
“Wani abin takaicin ma shi ne kwalaben da za a sa wannan (samfurin) babu su isassu, kuma ba za a iya sa wa a cikin wani waje ba in ba wadannan kwalabe ba,” a cewar gwamnan na Kano.
- An wayi gari da gawa yashe a gefen titi a Jihar Kano
- Coronavirus: PDP ta bukaci a yi bincike kan mutuwar mutane a Kano
Ya ce a gaskiya ba ma samun abinda ya kamata. “Gaskiya ba ma samun taimako da ma hadin kai daga shi wannan kwamitin na gwamnatin tarayya.”
Ganduje ya ce ya yi magana da jami’an gwamnatin tarayya a matakai daban-daban, amma har yanzu babu wani sakamako.
“Na yi magana da sakataren gwamnati, na yi magana da mataimakin shugaban kasa da kuma wasu mukarrabai, kamar shi minista na kiwon lafiya, na yi magana da su”
Gwamna Ganduje ya ce amsar da ya ke samu ita ce za a yi wani abu a kai, “amma har yanzu ban ga komai a kai ba,”in ji shi.
Martanin gwamnatin tarayya
Gwamna Ganduje ya musanta zargin cewa gwamnatinsa ba ta shirya wa yaki da cutar ta korona ba, inda ya ce jihar tana da cibiyoyin killace masu dauke da cutar har guda uku, sannan suna da isassun ma’aikatan lafiya.
To amma ya ce ba bu abinda ma’aikatan lafiyar za su iya yi fiye da karbar samufurin wadanda ake tunani suna dauke da cutar.
To sai dai a na sa bangaren, kwamitin shugaban kasa na kat ta kwana kan yaki da cutar korona ya musanta zarge-zargen da gwamnan na Kano ya yi.
Babban jami’i na kasa kan yaki da cutar korona a Dr. Aliyu Sani ya ce suna aiki da gwamnatin Kano kan yunkurin shawo kan cutar.
Ya ce dole ce ta sa aka rufe dakin gwajin cutar kwaya daya a Kano, saboda uku daga cikin ma’aikatan da ke gwajin sun kamu da cutar, sannan an killace sauran duka ma’aikatan.
Dr. Aliyu Sani ya ce an yi wa dakin gwajin feshin kashe kwayoyin cuta, kuma dole ne a bar dakin zuwa wasu kwanaki kafin a ci gaba da aiki a cikinsa.
“Yanzu mun tura jama’a, akwai mutum biyar da suka isa Kano, gobe (Litinin) za a gama gyaran dakin gwajin, za su kunnan mashin din don su tabbatar komai yana tafiya daidai,” a cewar Dr Sani.
Dangane da zarge-zargen da gwamna Ganduje ya yi na yin watsi da Kano, Dr. Sani ya ce “a yanzu muna da wajen mutu 17 suna aiki tukuru tare da gwamnatin Kano, da suka hadar da ma’aikatan NCDC da ma’aikatan Hukumar Lafiya ta Duniya WHO.”
Ya kara da cewa, suna ma shirin mayar da wasu ma’aikatan dake Lagos zuwa Kano, ksancewar Lagos sun nakalci yaki da cutar.
Haka kuma Dr. Sani ya ce kwamitinsu na shugaban kasa ya yi taro da wasu jami’an Amurka da na Majalisar Dinkin Duniya “za su tallafawa Kano,” kamar yadda ya fada.
Ana ci gaba da nuna damuwa Kan Kano
Yanayin da ake ciki a Kano din dai ya dauki hankalin kasar baki daya da ma duk wasu masana harkar lafiya.
Farfesa Sadiq Isa Abubakar shugaban cibiyar yaki da cuttuka masu yaduwa na asibitin Malam Aminu Kano da jami’ar Bayero, dan kwamitin yaki da cutar korona a jihar ne, ya ce halin da ake ciki a jihar yana ta da hankali.
“Halin da ake ciki hali na abin tsoro, bayan kwanaki da aka shafe ana yin gwaje-gwajen masu dauke da cutar korona, yanzu sai aka sami tsaiko.”
Ya kara da cewa: “Jinkirin da ake samu kafin a fitar da sakamakon yana tsoratar da mu ma’aikatan lafiya”.
Babban abinda ya fi daga hanakalin jama’a a yanayin da ake ciki na rashin sanin hakikanin illar da korona ke yi a jihar, da ma haske kan kiyasin mutanen dake dauke da cutar shi ne yawan mace-macen da ake samu a binin fiye da kowane lokaci a baya.
A cikin mako guda fitattun mutane da masu shekaru na kwanta dama a kusan dukkanin unguwannin jihar.
Cikin wadanda aka rasa daga Asabar zuwa Lahadi akwai farfesoshi guda hudu wanda na baya-bayannan shi ne Farfesa Balarabe Maikaba, na tsangayar nazarin aikin jarida a jami’ar Bayero dake Kano.
Abinda ke nan ya sa wasu masana harkar lafiya a wajen Kano ke nuna damuwa kan munin lamarin, kuma suke cewa da alama cutar korona ce ke wannan kisan mummuken.
Farfesa Usman Yusuf kwararren likita ne kuma tsohon shugaban inshorar lafiya na Najeirya.
“Duk inda ka ji wani dattijo ya mutu a ko ina a duniya – daga New York har Wuhan har Ghana – ko wace cuta ya ke da ita, yawanci za ka taras Covid-19 ce dalilin mutuwarsa.”
Ya ce, “Irin wadannan dattijan da dama suna fama da wasu matsalolin rashin lafiya, kamar ciwon sikari, hawan jini da cutar huhu, irinsu ta ke zuwa ta daka ta tafi mana da su”.
Yanayin da ake ciki dai a Kanon ya sa uwar jam’iyyar PDP ta kasa ta fitar da sanarwa tana mai cewa abinda ke faruwa a Kano abin takaici ne yadda gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta kasa daukar matakai na zahiri kan wannan batun mai tayar da hankali.
Daya daga jagororin PDP din a Kano Umar Haruna Dogowa ya ce a zahiri take cewa gwamnatin jihar ta gaza.
“Sauran jihohi kamar Legas da Ogun sun taka rawar gani kan yaki da wannan cutar, amma a jihar Kano babu wani abin a zo a gani da aka yi. Me yasa ba a samar da irin cibiyoyin bincike kamar yadda aka samar a wasu jihohin ba?”
Daya daya manyan abubuwan da suka fi daukar hankalin kan batun na Kano shi ne dakatar da gwajin cutar korona a cibiya daya tilo a Kano tsawon kwanaki.
To sai dai a yanzu a iya cewa matsalar ta kusa zuwa karshe, kamar yadda Dr. Isa Abubakar Aliyu daya daga cikin wadanda suke gwajin cutar ta korona a Kano ke cewa.
“Dama an kulle cibiyar ne domin a yi feshin magani. Feshin na daukar awa 48 kuma mun yi nasarar feshe ko ina.”
Ya ce ranar Litinin za a ci gaba da ayyukan gwaje-gwaje a cibiyar.
Masu lura da al’amura dai na cewa ya kamata Kano ta yi koyi da jihar Lagos da ta kafa cibiyoyin daukar samfurin gwaji a kowace karamar hukumar jihar, yayin da kuma ake da wuraren gwaji har uku, ta yadda za a samu hakikanin bayanin abinda ke faruwa a jihar ta Kano
Rahoton BBC HAUSA