Fitacciyar Jarumar masanaantar shirya fina finan Hausa ta Kannywood, Hauwa Waraka tayi Allah wadai ga masu bude shafukan Facebook da sunan ta har ma tayi yinkurin daukar mataki.
Jaruma Hauwa Waraka tace ita an bude shafukan a facebook da sunan ta har ma ana saka wasu maganganu da basu dace ba suna hada ni fada da mutane kuma hakan bai dace ba; inji ta
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa “War aka Tace”, ni ban taba yin Facebook ba bani da wani shafi ko kwara daya a kafar Facebook amma kuma an bude, duk mai yin wannan aikin ya dena.
Na rantse da girman Allah duk masu bude shafin facebook da suna na idan har na bibiye su na gane to wallahi Kotu ce zata raba ni da su, duk Wanda zai bude shafin Facebook ya bude da sunan sa.
Ta bayyana haka ne kunce cikin wani faifayin Bidiyon gargadi data wallafa, kuma Jaridar Dimokuradiyya ta Sami Faifayin Bidiyon.
Muna maraba da masu bukatar Faifayin Bidiyon don su kalla don tabbatarwa.