Babbar kotu a jihar Kano ta ɗage ci gaba da saurarar ƙarar da ɗan takarar gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya shigar ya na ƙalubalantar gwamnan Kano Abdullaji Umar Ganduje kan sayar da wasu daga cikin kadarorin gwamnati.
A yayin zaman kotun na yau, mai shari’a Nura Sagir ya ɗage saurar ƙarar, har zuwa ranar 29 ga watan Oktobar shekarar da muke ciki.
Lauyan Abba Kabir Yusuf, wato Bashir Yusuf Tudun Wuzirici ya ce matakin da gwamnan jihar Kano ya ɗauka na saida kadarorin gwamnatin ya saɓawa dokar tasarafi da filaye ta jihar Kano.
Ya yin da lauyan gwamnatin kwamishinan shari’ar Barrista Musa Abdullahi Lawal ya ce ƙorafin bashi da tushe ballantana makama.
Sai dai ya zuwa yanzu da muke haɗa wannan rahoto, wakilinmu ya kasa samun tattaunawa da masu magana da yawun ɓangarorin biyu domin jin ta bakinsu.