FG ta mayar da Asibitin Ƙwararru na Birnin Kebbi zuwa Asibitin Koyarwa
Gwamnatin tarayya ta amince da Asibitin Ƙwararru da ke Birnin Kebbi zuwa Asibitin Koyarwa.
Jami’in Hulda da Jama’a na Asibitin Ƙwararru na Birnin Kebbi, Malam Abdulmuminu Bawa Yauri, ya tabbatar da ɗaukaka darajar wurin.
KARANTA WANNAN LABARIN:Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin a fitar da Naira Biliyan 1.6 domin a tallafawa manoman citta
Yauri ya bayyana cewa, mahukuntan asibitin karkashin jagorancin Dakta Aliyu Hamza Balarabe, sun yi maraba da matakin, tare da yin alkawarin bayar da cikakken goyon bayansu ga nasarar inganta Asibitin, inda ya ce an dauki wannan mataki ne domin kara fadada ayyukan kiwon lafiya ga al’ummar jihar Kebbi.
Ya ci gaba da cewa, wannan sabon matakin zai baiwa daliban jami’ar tarayya dake Birnin Kebbi, FUBK damar amfani da wannan wurin wajen gudanar da ayyukansu na likitanci da sauran bukatu na kiwon lafiya, inda ya ce, “Da wannan inganta da aka samu, an kara matakin da asibitin ya dauka domin ya dace da ka’idoji na babbar cibiyar.
Malam Abdulmuminu ya taya al’ummar jihar Kebbi murnar wannan gagarumin ci gaba da aka samu, inda ya nanata kudurin mahukuntan asibitin na ci gaba da bayar da tallafi da kuma gudanar da ayyukansu na hukuma a matsayin sabon asibitin koyarwa na jami’ar tarayya
A wani labarin kuma:Kotu ta ɗaure Sanata mai ci kan shaidar NYSC ta bogi
Wata babbar kotu da ke zamanta a Apo, Abuja, ta tasa keyar wani Sanata mai ci Benson Konbowei a gidan gyaran hali na Kuje bisa zarginsa da yin jabun takardar shedar bautar kasa, NYSC.
An gurfanar da Sanatan Bayelsa ta tsakiya a gaban mai shari’a Christopher Oba a ranar 26 ga Maris, 2024.