Wata babbar kotun jihar Benue da ke zamanta a Makurdi a ranar Larabar da ta gabata ta hana gwamnatin jihar Benue ci gaba da shirinta na mayar da kamfanin sufuri mallakin gwamnatin jihar da aka fi sani da “Benue Links” zuwa na Yan kasuwa.
Kotun ta ba da wannan hukunci ne a cikin takardar neman odar wucin gadi da kungiyar Amalgamated Union of Public Corporations, Civil Service, Technical and Recreational Services Employees (AUCTPRE) da wasu mutane uku suka shigar har sai an yanke hukuncin a kan sanarwar.
Wadanda ake kara sun hada da gwamna Samuel Ortom da babban lauyan jihar da wasu mutane uku.
Wakilin Jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa, a watan Agusta gwamnatin jihar ta sanya 25 daga cikin kadarorinta na jama’a da aka ware a matsayin barauniyar hanya domin sayarwa, ciki har da Kamfanin sufuri na jihar wato Benue Links.
Mai shari’a Theresa Igoche ta bayar da wannan umarni ne bayan sauraron karar da lauyoyin masu shigar da kara, Imoter Gbim-Gbande, tare da kuma sanya ranar 3 ga watan Disamban shekarar nan, a matsayin ranar da za’a ci gaba da Sauraron karar.