Rikicin cikin gida a babbar jam’iyyar hamayya ta PDP ya sake ɗaukar wani sabon salo a jiya Litinin a jihar Rivers
Bayan da Wata babbar kotu a jihar ta dakatar da Shugaban jam’iyar na kasa Uche Secondus daga bayyana kansa a matsayin shugaban PDP na kasa.
Secondus, wanda yake ta bakin kokarin shi na ganin ya ci gaba da rike mukaminsa, an ba shi damar ya shirya gangamin taron jam’iyyar a watan Oktoba a baya.
Sai dai rahotannin da Jaridar Dimokuradiyya ke samu na nuna cewa, Secondus ya bukaci cewa, dole a barshi ya karisa wa’adin mulkinsa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jami’an soji sun kubutar da mutane 15 a Kaduna
Mai shari’a O. Gbasam, ya tumbuke Uche Secondus daga matsayin shugaban PDP yayin da yake yanke hukunci kan karar da jiga-jigan jam’iyar suka shigar a kansa.
Tunda faridai Waɗanda suka shigar da karar sun haɗa da, Ibeawuchi Ernest Alex, Dennis Nna Amadi, Emmanuel Stephen da kuma Umezirike Onucha
A lokacin yanke hukuncin, Alkalin kotun ya kuma hana Secondus jagorantar shirya gangamin taron PDP na gundumomi da da kananan hukumomi.
“Kotu da bada umarnin hana wanda ake kara bayyana kanshi a matsayin shugaba ko kuma gudanar da ayyukan shugabancin jam’iyar .” Inji shi.
“Hakanan kotu ta umarci hana wanda ake kara kira, halarta, ko jagorantar wani taro ko shiga wani kwamiti a matakin gunduuma, karamar hukuma, ko na jiha.” A cewar Alkalin.
Kazalika ya ce, “Kuma an hana wanda ake kara daga shirya gangamin taron gundumomi, kananan hukumomi, ko na jihohi, yayin da aka dakatar da shi daga kasance wa dan jam’iyyar.”
Comments 1