Wata Kotun Majistare ta 3 da ke zamanta a Jihar Bauchi, karkashin jagorancin mai shari’a Ahmed Musa, a ranar Talata, ta tasa keyar mawallafin Jaridar WikkiTimes, wani kamfanin yada labarai na yanar gizo a jihar, Haruna Mohammed gidan yari, bisa tuhumarsa da laifin “haifarwa jama’a hargitsi da cin fuska ga Gwamna. Bala Mohammed.
Kwafin zarge-zargen da ake yi wa Haruna mai shekaru 32, wanda wakilinmu ya gani bayan sauraron karar a ranar Talata, ya nuna cewa wanda ya shigar da karar, kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, Aminu Alhassan, ya zargi dan jaridar da daukar wasu mata haya domin tada hankalin jama’a. tare da tunzura su da yin kalaman da za su kawo illa ga zaman lafiya da walwalar masu kada kuri’a a mazabar Duguri da ke karamar hukumar Alkaleri da kuma bata sunan Gwamna mai ci a unguwar sa sabanin sashe na 114 na kundin laifuffuka.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hotuna: Tinubu Ya Karbi Bakuncin Goodluck Jonathan da Sauran Wakilan ECOWAS
Sai dai kuma lokacin da aka ambaci karar a kotu, wanda ake tuhumar ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa.
Haruna Mohammed, daga ma’aikatar shari’a, ya sanar da cewa babban mai shigar da kara na jihar na son karbe shari’ar daga hannun ‘yan sanda tare da ci gaba da aiki da ita kamar yadda yake kunshe a kundin tsarin mulki na shekarar 1999 da aka yi wa gyara.
Alkalin kotun ya dage sauraron karar zuwa ranar Laraba, 1 ga watan Maris, 2023 don ba shi damar yanke hukunci kan bukatar neman belin da lauyan wanda ake tuhuma, SG Idrees ya shigar.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa an kama dan jaridan ne a garin Duguri, mahaifar gwamnan a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu, yayin da yake gabatar da rahoton zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya, kuma an kai shi sashin binciken manyan laifuka na ‘yan sanda kafin gurfanar da shi a ranar Talata a gaban Kotu.
Ana ci gaba da tsare shi a gidan yari na Najeriya dake Bauchi, har zuwa lokacin da za a yanke shawarar neman belinsa.
A halin da ake ciki, rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, ta tabbatar da kama dan jaridar tare da tsare shi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Ahmed Wakil, Sufeto na ‘yan sanda, ya tabbatar da kamun a wata hira da manema labarai ta wayar tarho a jihar a ranar Talata.
Ya ce: “Hakika ‘yan sanda sun samu korafin cewa wani dan jarida na tunzura jama’a a babban zaben da aka yi ranar Asabar.
“Wannan shine dalilin da ya sa muka gaggauta shiga tsakani don tabbatar da cewa mun kiyaye doka da oda, musamman a wannan lokacin.”
A wani labarin kuma,PDP Tayi Watsi Da Sakamakon Zaben 2023 a Jihar Borno
Jam’iyyar PDP a yankin Borno ta tsakiya ta yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka kammala a baya bayan nan saboda kura-kuran zabe da kuma kin shigar da sakamakon zabe daga rumfunan zabe zuwa BVAS da hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC tayi bisa ka’idojin Dokar Zabe na 2022.
An bayyana hakan ne a ranar Talata a cibiyar NUJ da ke Maiduguri yayin wata sanarwar hadin gwiwa da dan takarar kujerar Sanatan Borno ta tsakiya na jam’iyyar PDP Barista Umara Kumalia da wasu ‘yan takarar majalisar wakilai daga kananan hukumomi takwas da ke shiyyar suka sanya wa hannu.