Wata kotu a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar ta yanke hukuncin daurin wata guda da kwanaki bakwai na zaman gidan kaso ga wata ‘yar jaridar wadda ke yin sharhi a kan al’amura ta intanet.
Gidan Rediyon Jamus ya labarto cewa; A cikin watan Yuni da ya gabata ne aka kama Samira Sabou bayan da dan shugaban kasar Nijar ya shigar da kara a gaban kotu a kan abin da ya kira labaran karya da ya ce Samira ta wallafa dangane da batun cinikin makamai cewar wani dan kasuwar ya karbi kwangilar da aka yi cin hanci a ciki da sunan dan shugaban kasar.
Tuni dai da Samira ta kwashe sama da kwanaki 20 a gidan kason wacce ake tsare da ita tun 10 ga watan Yuni.