Babbar Kotun Tarayya dake zamanta a Jalingo a ranar Talata ta kori Shuwagabannin Jam’iyyar APC a Jahar, bayan ta bayyana zaɓen da yayi su bai halatta ba.
A yanke Shari’ar sa na tsawon awanni uku, Joji Mai Kula da shari’ar, Mai Shari’a Simon Amobeda ya ƙalubalanci yanda aka gudanar da zaɓen, kuma ya umarce su dasu daina nuna kansu a matsayin Shuwagabannin Jam’iyyar a Jahar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Majalisa tayi Watsi da kudurin warewa Mata kujeru na musamman
“Daga abunda jam’iyya ta gabatar, masu ƙarar ba’a basu damar yin zaɓen ba wanda ya gudana a watan Oktoba na Shekarar 2021.
A dalilin haka, Jam’iyyar ta karya dokar kundin tsarin mulkin ta, na ƙin bin dokoki. A saboda haka an rusa zaɓen.”
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta The PUNCH ta bada rahoton cewa, wasu Fusatattun ƴaƴan Jam’iyyar sun kai ƙara a Kotu akan cire su daga yin zaɓen.
Dayake maida jawabi, Lauya mai Kare Ƙarar John Odekina Esq ya bayyana ƙudirinsu na ɗaga ƙarar zuwa Kotun Gaba.
Mai Shigar da Ƙarar Joy Ezekiel Esq Wanda ya bayyana jindaɗi akan wannan hukunci, yace Kotu itace abu na ƙarshe ga marar ƙarfi.
Alhaji Ibrahim Tukur El-Suldi, Shugaban Jam’iyyar APC a Taraba ba’a same shi a waya ba, domin bai ɗaga kira ba, ko kuma maida saƙon da aka yi mashi.