Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Jalingo a jihar Taraba ta kori Emmanuel Bwacha a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Daily Trust ta ruwaito cewa, A hukuncin da ya yanke ranar Talata, Mai shari’a Simon Amobeda ya soke zaben fidda gwani wanda ya samar da Bwacha a matsayin dan takarar jam’iyyar APC a jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sarki Charles III Ya Ketare Zuwa Scotland Jim Kadan Da Binne Mahaifiyarsa
Alkalin kotun ya hana Bwacha bayyana kansa a matsayin dan takarar gwamna a jam’iyyar APC sannan ya umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da karta amince da Bwacha a matsayin dan takara.
Ya ba da umarnin a gudanar da sabon zaben fidda gwani na gwamna a jihar nan da kwanaki 14 masu zuwa.
Dama dai David Sabo Kente, daya daga cikin wadanda suka tsaya takara a zaben fidda gwanin da aka soke ne ya shigar da kara a kan takarar Bwacha.
A WANI LAVARIN KUMA: Da Yawan Ɗalibai Mata Sun Yi Ciki, Maza Kuma Sun Koma Kanikanci Inji NANS
Kungiyar dalibai ta kasa NANS, ta caccaki gwamnatin tarayya kan yajin aikin watanni bakwai da kungiyar malaman jami’o’i, ASUU ta shiga.
NANS ta ce yajin aikin na barazana ga ‘yancin dan Adam na daliban Najeriya, dangane da samun damar karatu.