Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da sabuwar bukatar bayar belin da DCP Abba Kyari da aka dakatar ya daga aikin.
Mai shari’a Emeka Nwite, a hukuncin da ya yanke, ya ce Mista Kyari bai bayar da isassun dalilan da za a amince da bukatarsa ba, don ganin an bada shi a hannun beli.
Alkalin ya ce dan sandan da ake tsare da shi ya kasa kawo sabbin bayanai a sabuwar bukatarsa bayan an ki amincewa da bukatar belin da aka yi masa a baya.
KARANTA ANAN: ‘Yan Sanda Sun Kama Wasu ‘Yan Bijilanti 2, Da Wani Bisa Zargin Cin Zarafin Mata
Sakamakon haka Mista Nwite ya dage sauraron karar har zuwa ranar 19, 20 da 21 ga watan Oktoba domin ci gaba da shari’ar.
A ranar 20 ga watan Yuli ne mai shari’a ta tsayar da ranar da za ta yanke hukunci kan karar belin da Mista Kyari da wasu jami’an ‘yan sanda suka shigar da hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, da laifin safarar miyagun kwayoyi.
Mista Kyari dai ya roki kotu da ta sake duba batun belinsa bayan harin da ‘yan ta’adda suka kai a gidan gyaran hali na Kuje inda suka kubutar da mambobinsu da dama.
Hakan ya faru ne yayin da Kyari da sauran wasu manyan mutane ke tsare da a gidan yarin Kujen.
A wani labari kuma: Jami’an KAROTA Sun Kama Wata Tirela Maƙare Da Giya
Hukumar kula da Zirga-zirga Ababen Hawa ta jiha KAROTA ta cafke wata mota ƙirar Tirela maƙare da Giya, lokacin da ake shirin Kaita masaukinta a Jihar Kano.
Jami’an hukumar KAROTA ne suka sami nasarar cafke motar, lokacin da Direban ke yunƙurin shigowa cikin jihar Kano da misalin karfe 3:00na dare.