pdp

Kotu Ta Soke Zaben Dan Majalisar PDP A Kaduna

Kotun sauraren kararrakin zaben ‘yan majalisa a jihar Kaduna a ranar Asabar ta soke zaben dan majalisar jihar mai wakiltar Kagarko, inda ta bukaci da a sake zabe a rumfuna 22 a mazabar.

Soke zaben ya biyo bayan karar da aka kai Morondia Tanko na PDP, a zaben 9 ga watan Maris inda aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

Nuhu Shadalafiya tsohon mataimakin shubaban majalisar jihar Kaduna, kuma dan takarar APC shi ne ya kalubalanci nasarar dan majalisar PDP din.

Shugaban kotun sauraren kararrakin zaben, mai shari’a Adamu Suleiman, a yayin da yake yanke hukunci ya nemi da a sake zabe a mazabu 22 a tsakanin gundumomi biyu na yankin.

Mai Shari’a Maimuna Abubakar ita ce ta karanto hukuncin, inda ta ce mai shigar da karan ya gamsar da kotun da hujjoji shiyasa kotun ta soke zaben.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *