Wata kotu da ke Abuja ta yanke hukuncin daurin shekaru biyar a gidan kaso kan wani mai sayar da nama mai suna Bilia Zakari, bisa samun sa da laifin aikata laifuka, cin zarafi da cutarwa da kuma sata a yankin Jiwa, na garin Abuja.
Tun da farko dai, mai gabatar da kara, Ocho Jacob, ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargin a ranar 2 ga watan Fabrairu, ya kai wa mai karar, Awele Ruth hari a kan hanyarta ta zuwa wurin aiki, inda ya raunata a hannunta tare da kwace jakarta mai dauke da waya da wasu kayayyaki masu daraja.
Wanda ake zargin ya amsa laifukan da ake tuhumarsa da shi.
Kazalika Alkalin kotun, Muhammed Adamu Wakili, ya ce hukuncin zai zama izina ga Yan baya.