By Abbas Yakubu Yaura
Wata babbar kotun jihar Kano karkashin jagorancin mai shari’a Jamilu Shehu ta yankewa wasu masu fasakwaurin katin ATM guda uku hukuncin dauri a gidan yari na tsawon watanni shida kan kowannensu bisa wasu tuhume-tuhume guda uku da ake yi musu.
Jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC sun kama wadanda ake zargin Abdullahi Usman, Musa Abubakar da Abdulwahid Auwalu tsakanin 24 ga watan Nuwamba zuwa 1 ga watan Disamba, 2021.
Bayan da aka kama su, an gano cewa Musa Abubakar, wanda ke kan hanyarsa ta zuwa Dubai (UAE) ya boye katunan ATM guda 714 a lokacin da Abdullahi Usman ya nufi kasar Saudiyya, shi kuma yana dauke da katin ATM guda 298 a hannunsa.
A daya bangaren kuma an kama Abdulwahid ne da katin ATM 132 a lokacin da yake kokarin shiga jirgin Ethiopian Airlines zuwa birnin Istanbul na kasar Turkiyya.
Wadanda ake tuhumar sun amsa laifukan nasu daban-daban lokacin da aka karanta musu, kuma lauyan masu shigar da kara, Barista Usman Shehu, ya bukaci kotun data yanke musu hukunci.
Bayan sauraron rokon jinkai daga lauyan da ake kara, Barista A.M Bashir, Mai shari’a Shehu ya yankewa wadanda ake kara hukuncin daurin watanni shida a gidan yari tare da zabin biyan tarar Naira 50,000 ko wannen su.