Kotu ta yiwa matashi ɗaurin rai da rai kan yin Luwaɗi da ƙaramin yaro
Kotun jihar Jigawa ta yankewa wani matashi dan shekara 25 hukuncin daurin rai da rai bisa samunsa da laifin yi wa wani yaro dan shekara 10 luwadi.
Mai shari’a Musa Ubale ne ya yanke wa matashin mai suna Aminu Ali hukunci.
KARANTA WANNAN LABARIN:Kotu ta ɗaure Sanata mai ci kan shaidar NYSC ta bogi
Ali, mazaunin unguwar Aukayawa a karamar hukumar Gwaram a jihar, an same shi da laifi ne bayan da masu gabatar da kara suka gabatar da shaidu biyar tare da gabatar da shaidu hudu, ciki har da rahoton likita, inda suka tabbatar da laifinsa “baya da wata shakka.”
Masu gabatar da kara sun yi nasarar cewa Ali ya yaudari wanda aka azabtar ya kuma yi lalata da shi.
Mai shari’a Ubale, a hukuncin da ya yanke, ya bayyana cewa, da gaske masu gabatar da kara sun tabbatar da shari’ar ba tare da wata shakka ba.
Sakamakon haka, kotu ta yanke wa Ali hukuncin daurin rai da rai a karkashin sashe na 3 (2&4) na dokar hana cin zarafin mutane ta jihar Jigawa (VAPP LAW).
Alkalin ya kuma sanar da wanda ake tuhuma hakkinsa na daukaka kara a cikin watanni uku
A wani labarin kuma:FG ta mayar da Asibitin Ƙwararru na Birnin Kebbi zuwa Asibitin Koyarwa
Gwamnatin tarayya ta amince da Asibitin Ƙwararru da ke Birnin Kebbi zuwa Asibitin Koyarwa.
Jami’in Hulda da Jama’a na Asibitin Ƙwararru na Birnin Kebbi, Malam Abdulmuminu Bawa Yauri, ya tabbatar da ɗaukaka darajar wurin.