Kotun ECOWAS ta yanke hukunci, tace Kulle Twitter ya saɓawa Doka, ta gargaɗi Najeriya kan sake aikata wa
Kotun ECOWAS ta ayyana cewa Najeriya dakatar da Twitter da Gwamnatin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a matsayin abinda ya saɓawa Doka, ya umarci Gwamnati da kada ta sake yin haka.
Wannan na zuwa ne akan wata ƙara da Ƙungiyar Kare Tattalin Arziki ta shigar da wasu ƴan Najeriya 176.
KARANTA WANNAN LABARIN: APC ce ta biyani maƙudan kuɗaɗe domin in goyi bayan Tinubu — Mawaƙi Portable
Idan za’a tuna bayan goge rubutun Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, Ministan Yaɗa Labaru da Al’adu, Lai Mohammed ya sanar da dakatar da Twitter a Najeriya.
Gwamnati ta kuma yi gargaɗin kamawa tare da zartar da hukunci ga duk wanda aka kama yana amfani da shafin Twitter a Kasar, a yayinda Hukumar Kula da Kafafen Yaɗa Labaru ta umarci dukkanin Kafafe dasu daina amfani da shafin Twitter.
Amma a hukuncin da aka yanke a ranar Laraba, Kotun ECOWAS ta bayyana cewa tana da damar da zata saurari Shari’ar, kuma zata yanke hukunci akan haka.
Kotun ta yanke hukunci cewa kulle harkokin Twitter ya saɓawa Doka, Kuma ya saɓawa Doka ta 9 ta Hakkin Ɗan Adam ta Nahiyar Afirka da sauran Hukumomin Kare Hakkin Bil’adama.
Kotun ECOWAS ta bada umarni ga Gwamnati data biya wasu kuɗaɗe, sai kotun ta umarci Mataimakin Magatakarda daya tattara kuɗaɗen da zata biya.