Kotun kolin Kenya na shirin gudanar da wani taron share fage kan kararrakin da ke neman soke sakamakon zaben shugaban kasar. Kamar yadda BBC ta ruwaito.
A makon da ya gabata ne aka gabatar da koke-koke guda tara na neman soke nasarar William Ruto.
Rahotanni sun bayyana cewa taron zai tattauna jerin batutuwan da kotun za ta tantance tare da yanke hukunci a ranar Litinin ami zuwa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaban Kasa Buhari Ya Gana Da Gwamnonin Jam’iyyar APC
Wadanda aka shigar da Kararrakin su, Sun hada da shugaban hukumar zaben Wafula Chebukati da ake zargi da karya doka ta hanyar ayyana Mista Ruto a matsayin wanda ya lashe zaben kasar ta Kenya.
Haka kuma za a yi la’akari da rarrabuwar kawuna da aka samu a hukumar zaben, inda wani bangare ke neman a soke sakamakon zaben, wani abngaren kuma ya ce a tabbatar da shi.
Taron dai zai samu halartar alkalai bakwai wadanda za su jagoranci karar da ta taso daga zaben na ranar 9 ga watan Agusta.
A WANI LABARIN KUMA: United Ta Cimma Matsayar Daukar Dan Wasa Anthony
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta cimma yarjejeniya kan sayen dan wasan gaban Brazil Antony daga Ajax.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa kungiyar kwallon ƙafan ta kasar Ingila ta sanar da hakan ne a yau Talata.