Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Talata ya gana da gwamnonin jam’iyyar APC a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC PGF, kuma gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Bagudu, ne ya jagoranci sauran gwamnonin wajen taron wanda ya dauki tsawon mintuna 30 ana gudanar da taron.
Wadanda suka halarci taron sun hada da Babajide Sanwo-Olu na Legas, Dr Kayode Fayemi na Ekiti, Abubakar Badaru na Jigawa, Dapo Abiodun na Ogun, Abubakar Bello, Inuwa Yahaya, Abdullahi Sule da mataimakin gwamnan jihar Ebonyi, Dr. Eric Igwe.
KARANTA ANAN: United Ta Cimma Matsayar Daukar Dan Wasa Anthony
Jaridar Dimokradiyya ta rawaito cewa har kawo yanzu ba a bayyana makasudin taron ba, kuma gwamnonin ba su yi wa manema labarai bayanin tattaunawar da suka yi ba.
A wani labarin kuma: Muna Allah Wadai Da Zuƙi Tamallen Ministocin Buhari – ASUU
Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta zargi wasu ‘yan majalisar zartarwa ta shugaban kasa Muhammadu Buhari da yi wa kungiyar karya a yayin da suke tattaunawa.
Kungiyar ta bayyana rashin jin dadin ta kan karyar da Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu da Ministan Kwadago Chris Ngige da takwaransa wanda shi ne Karamin Minista Festus Keyamo (SAN) suka yi kan wasu batutuwan da suka shafi bukatun ta.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Farfesa Emmanuel Osodoke ya sanya wa hannu a ranar Litinin.