A yau juma’a ce, Kotun daukaka kara ta kasar Kenya, ta amince da hukuncin da ya gabata cewa, canje -canje masu rikitar wa ga kundin tsarin mulkin kasar da Shugaba Uhuru Kenyatta ke jagoranta ba bisa ka’ida ba ne.
Mai shari’ar Kotun Daniel Musinga ne ya bayyana hakan lokacin da ake zanman sauraran karar.
Inda ya bayyana cewa, “Shugaban kasa ba shi da iko a karkashin tsarin mulki don fara sauye -sauye ga kundin tsarin mulkin,” in ji shugaban kotun Daniel Musinga.
KARANTA WANNAN LABARIN: Daliban Kaduna dake karatu a Kasashen ketare sun ziyarci Gwamnan da Sanata Uba Sani
Kazalika ya ce “Majalisar dokokin kasar ce kawai, za ta iya yin kwaskwarimar tsarin mulkin kasar,” a cewar shi.