Kuɗin kyauta, da Albashi baza su isheku rayuwa ba — Adeyanju ga Ƴan Najeriya
Dan rajin kare hakkin dan Adam, Deji Adeyanju ya shaidawa ‘yan Najeriya cewa kudin kyauta da albashin wata ba su isa ba ga rayuwar mutum.
Ya bukaci ‘yan Najeriya da su shiga sana’o’in da za su rika samun kudaden shiga akai-akai.
KARANTA WANNAN LABARIN: Najeriya Ba Ta Bukatar Dan Takarar LP, Kirar Sunan Shi Ma Abun Kunya Ne—- Tinubu
Adeyanju ya bayyana haka ne a ranar Asabar a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
“Ku sami kasuwancin da ke kawo kudin shiga yau da kullun komai kankantarsa. Kuɗin kyauta ba ya dorewa. Albashi kuma ba zai iya sa ka arziƙi ba, ka fara kasuwanci a yau,” in ji shi.
Bayanai daga Hukumar Kididdiga ta Kasa, Multidimensional Poverty Index Report, da aka fitar kwanan nan, sun nuna cewa har yanzu ‘yan Najeriya miliyan 133 ne ke fama da talauci, wanda ke wakiltar kashi 65 na daukacin al’ummar kasar.
Bugu da kari, GDP na Najeriya, ya ragu da kashi 2.25 na baya-bayan nan, shi ma ya kara tabarbarewar yanayin talauci na yawancin ‘yan kasar.
Wadannan alkalumman tattalin arziki na nuni da gwagwarmayar yau da kullum da ‘yan Najeriya ke yi.
A wani labarin kuma: Ku Ƙwato Najeriya daga hannun Miyagu, Obi ga Matasa
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya kalubalanci matasan Najeriya da su kwato Najeriya daga hannun gurbatattun shugabanni su samar da kasar da suke so kuma da za su yi alfahari da ita.
Obi ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a wani taron matasa na kasa da kasa a Enugu mai taken; ‘Yin amfani da lokaci don tsara makomar gaba’.