Hukumar Hisbah a Kano sun yi kira ga al’umma da su rika kai rahoton duk inda suka ga karuwai domin bayyana ayyukan karuwan a inda suke domin ganin an dakile su don ci gaban jihar. Wannan sanarwar ta fito ne daga jami’in hulda da jama’a na hukumar, Alhaji Lawan Ibrahim ga manema labarai a ranar Laraba a Kano.
Kwamandan hukumar, Sheikh Harun Ibn-Sina ya yi wannan kiran ne a cewar sanarwar a yayin da yake yiwa wadansu mata jawabi wadanda aka kama akan tituna da daddare a cikin garin na Kano.
Ibn-Sina ya ce hukumarsu ba za su bari ana aikata laifuka a jihar ba, za su yi iya bakin kokarinsu wajen ganin sun dakile rashin da’a a jihar musamman ma harkar karuwanci. Ya tabbatar da cewa wadanda aka kama a yayin samamen ‘yan mata ne.
Ya ci gaba da cewa; an gudanar da samamen ne a Church Road Sabon Gari, Railway quarters, Tukur road a karamar hukumar Nassarawa GRA da Sarkin Yaki Road a Kano.