Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya da su rika bin ka’idojin manyan tituna na kasar nan a ko da yaushe.
Buhari ya bayyana hakanne a cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar ayyuka da gidaje ta tarayya Boade Akinola ya fitar a ranar Juma’a a lokacin kaddamar da titin Sokoto-Tambuwal-Kontagora-Makera mai tsawon kilomita 304km.
Shugaban wanda ya samu wakilcin babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami (SAN), ya ce gwamnatinsa ta dukufa wajen cika alkawarin da ta dauka na baiwa ‘yan Najeriya hanyoyin masu inganci.
An ambato shugaban kasar ya lissafta sabawa dokokin hanha, da suka hada da lodin wuce kima da ababen hawa da manyan motoci keyi, da dai sauran su.
Tun da farko, Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, ya zayyana wasu hanyoyin da nan ba da dadewa ba za a fara aiki a fadin kasar nan da su hada da sashe na biyu da ke da nisan kilomita 142.2 x 2 (dual) tsakanin Shuwarin da Azare, wadanda suka hada jihohin Jigawa da Bauchi; Sashe na uku wanda ya shafi kilomita 106.3 x 2 tsakanin Azare da Potiskum, wanda ya hada jihohin Bauchi da Yobe; Titin Vandeikya-Obudu Cattle Ranch Road wanda ke da nisan kilomita 24 da ya hada jihohin Benue da Cross River da kuma titin Nnawe-Uduma-Uburu mai nisan kilomita 26.27, sai Kuma mai nisan kilomita 14 zuwa Ishiagu mai da ta hada da jihohin Enugu da Ebonyi.
Sanata mai wakiltar Kebbi ta tsakiya kuma shugaban kwamitin ayyuka na majalisar dattawa Sanata Adamu Aliero, ya ce tun da aka gina hanyar a shekarar 1973 ba a yi wani gagarumin gyara ba har hanyar taa zama tarkon mutuwa ga Matafiya..
Anashi bangaren Mai martaba Sarkin Yauri, Dr Muhammad Zayyanu Abdullahi, ya ce gyaran hanyar na da matukar muhimmanci ga ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin al’umma da kuma makwabtan kasashen ECOWAS.
Comments 1