Masu garkuwa da shugaban makaranta, mataimakin shugaban makaranta, da malaman Shirin N-Power uku na makarantar Auga Community Grammar da ke yankin Akoko a jihar Ondo sun bukaci a biya su Naira miliyan 35 domin a matsayin kudin fansa kafin su sake su.
Uwargidan shugaban makarantar, Mrs Hellen Adeyemi, wacce ta tabbatar da hakan a wata tattaunawa ta wayar tarho, ta ce, ba su da karfin tara Nair Milliyan 35 domin amso wadanda aka sace.
Idan za’a iya tunawa dai, An dai yi Garkuwa da Shugaban makarantar Mai suna Joshua Adeyemi; da mataimakinsa Ifedayo Yesufu da malaman Shirin N-Power 3 ne a ranar Alhamis din da ta gabata da rana, a lokacin da suke tafiya a cikin wata mota kirar Toyota Corolla a kan titin Auga zuwa Ise a karamar hukumar Akoko ta Gabas.
Daya daga cikin malaman da aka sace mai suna Misis Blessing Okeke, wacce ke da juna biyu, an sake ta daga bisani.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ku Guji Sabawa Dokokin hanya–Shugaba Buhari Ga Yan Nigeria
Jami’in ‘yan sanda na shiyya ta Ikare, SP Oladutoye Akinwande, ya bayyana cewa an fara gudanar da bincike domin ceto wadanda abin ya shafa.
A halin da ake ciki, wasu mazauna Akoko musamman garuruwan Ajowa, Isua, Akunu, Auga, Ikakumo, Igashi da Eriti sun yi kira ga gwamnati da ta kara tsaurara matakan tsaro a yankunan saboda yawaitar laifuffukan da ake samu sakamakon rage shingayen binciken sojoji daga tituna a jihar.