Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta kama wata mata ‘yar shekara 30 a lokacin da take kokarin kai harsashi guda 991 zuwa sansanin wani fitaccen shugaban ‘yan bindiga da ke cikin jerin sunayen da jami’an tsaro ke nema ruwa a jallo.
Wacce ake zargin mai suna Fatima Lawali, tana kan hanyarta ne daga Sokoto domin kai wa wani dan fashi da makami mai suna Ado Alero, wanda ya yi kaurin suna a dajin Zamfara, inda aka kama ta a unguwar Gada Biyu a karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ayuba N. Elkanah ne ya baje kolin wacce ake zargin tare da wasu a ranar Juma’a a hedikwatar rundunar dake jihar.
An ruwaito cewa, Fatima ‘yar asalin karamar hukumar Kaura Namuda ce ta kware wajen samar da makamai da alburusai ga ‘yan bindiga da ke aiki a jihohin Arewa maso Yamma.
Shugaban ‘yan sandan yayin da yake baje Kolin wacce ake zargin ya ce: “Fatima Lawali ‘yar asalin karamar hukumar K/Namoda ta kware wajen samar da makamai da alburusai ga ‘yan bindiga a jihohin Zamfara, Sokoto, Kebbi, Kaduna, Katsina da Neja.”
“Kuma an kama ta ne a unguwar Gada Biyu da ke karkashin karamar hukumar Bungudu dauke da harsashi Bindiga kirar AK-47 har guda dari tara da casa’in da daya (991) daga kauyen Dabagi da ke jihar Sokoto, domin kai su ga wani babban dan fashin nan mai suna Ado Alero da ke ta’addanci a jihar Zamfara da wasu jihohin da ke makwabtaka da ita. Ana ci gaba da bincike.”