Shugaban kasar Poland Andrzej Duda ya gargadi kasashen Afirka da su yi taka-tsan-tsan da abin da ya kira manufofin Rasha game da nahiyar.
Yayi wannan kiran ne a wata hira da yayi da kafar yada labarai ta BBC.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Tsare Wani Matashi A Gidan Yari, Bisa Daba wa Mahaifiyarsa Wuka A Fuska
Da yake zantawa da BBC, Mista Duda ya ce karuwar tasirin da Rasha ke da shi a Afirka ta fuskar tsaro da makamashi wani sabon yunkuri ne na mulkin mallaka.
Ya yi iƙirarin cewa Kremlin na amfani da rukunin Wagner wanda wani kamfani mai zaman kansa na tsaro a matsayin taimakawa kasashen Afrika da kayan aikin soja a Nahiyar.
Rahotanni sun nuna cewa shugaban na Poland ya ziyarci wasu kasashen Afirka uku da suka hada da Najeriya, Senegal da kuma Ivory Coast a wani yunƙuri na inganta dangantakar da ke tsakanin kasar da kasashwn nahiyar Afrika da kuma lalubo hanyoyin da ba za a iya dai na amfani da man fetur da iskar gas din Rasha, sakamakon rikicin makamashin da duniya ke fuskanta.
Idan ba’a manta ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov a watan Yuli ya nuna irin rawar da kasar ke taka a fannin diflomasiyya a nahiyar Afirka a ziyarar da ya kai kasashen Masar da Habasha da Uganda da kuma Kongo Brazzaville.
Sai dai a watan Oktoba mai zuwa ne za a gudanar da taron koli na Rasha da kasahsen dake yankin nahiyar Afirka karo na biyu a kasar Habasha, inda za a rattaba hannu kan yarjejeniyoyin kasuwanci da tsaro domin karfafa alakar Rasha da nahiyar Afrika.
A WANI LABARIN KUMA: An Sako Fasinjoji Hudu Da Aka yi Garkuwa Da Su A Jihar Rivers
Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ta tabbatar da sakin mutane 4 daga cikin fasinjojin da aka yi garkuwa da su a kan titin Emohua/Kalabari na hanyar da ta hada yankin Gabas da Yammacin jihar a ranar Asabar din da ta gabata.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Grace-Iringe-Koko, wadda ta bayyana hakan a Fatakwal a ranar Talata, ta ce an sako mutanen ne a daren ranar Litinin.